Ba za mu bayyana sakamakon bincike kan harin da Amurka ta kawo ba — ’Yan Sanda

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, ta ce tana da bayanai game da harin da Amurka ta kai wa ’yan bindiga a wasu sassan Jihar Sakkwato, amma ba za ta bayyana bayanan ga jama’a ba.

Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ne, ya bayyana haka yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels, a ranar Talata.

Ya ce rundunar ta san abin da ya faru a hare-haren, amma ba ta da niyyar yin ka5rin bayani a wannan lokaci.

Hundeyin, ya ƙara da cewa an tura jami’an ’yan sanda zuwa yankunan da abin ya shafa domin tabbatar da tsaro.

Ya ce hakan ya zama dole musamman saboda rahotannin da ke nuna cewa harin ya shafi wasu fararen, inda wasu suka rasu, sannan wasu suka jikkata.

A ranar 25 ga watan Disamba, 2025, Amurka ta kai hari kan ’yan bindiga a Jihar Sakkwato.

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta ce harin ya yi sanadin mutuwar wasu ’yan bindiga da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar IS, kuma an kai harin ne da amincewar Gwamnatin Najeriya.

Haka kuma, rundunar sojin Amurka a Afirka (Africom), ta sanar cewa ta bai wa Najeriya wasu kayan aikin soji domin taimakawa wajen yaƙi da matsalar tsaro.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *