Gwamnatin Kano Ta Haramta Yanka Dabbobi Masu Ɗauke da Juna Biyu A Jihar
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta yanka dabbobi masu ɗauke da juna biyu, tana mai jaddada cewa duk wanda aka samu ya karya dokar zai fuskanci hukunci.
Sanarwar ta fito ne ta hannun Kwamishinan Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo da Albarkatun Dabbobi ta Jihar Kano, Dakta Aliyu Isa Aliyu, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 4 ga Fabrairu, 2026.
- Mutane 597 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Cikin Wata 1 — FRSC
- Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Rasha Ta Kafar Bidiyo
A cewar kwamishinan, dokokin ma’aikatar sun tanadi haramta yanka kowace dabba da ke ɗauke da ciki, tare da shimfiɗa hukunci ga duk wanda aka samu ya aikata hakan.
“A cikin dokokin Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo da Albarkatun Dabbobi ta Jihar Kano, an haramta yanka dabbar da take da ciki, kuma akwai hukunci ga duk wanda aka samu da aikata hakan. Daga yanzu, dokar ta fara aiki,” in ji Dakta Aliyu Isa Aliyu.
Wannan matakin yana daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na kare lafiyar dabbobi, bunƙasa harkar kiwo, da tabbatar da dorewar samar da nama a jihar Kano.
An bukaci mahauta da masu kasuwancin nama da jama’a gaba ɗaya da su bi dokar, tare da haɗa kai da jami’an gwamnati domin tabbatar da aiwatar da ita yadda ya kamata.
[ad_2]
Source link