‘Zinariyar Arewa’ ta biya wa mutumin da aka kashe wa iyalai 7 a Kano aikin Hajji

[ad_1]



Wata attajira kuma ’yar gwagwarmaya, Hajiya Bilkisu Sulaiman Fema, ta biya wa Malam Haruna Bashir, magidancin nan da aka kashe wa mata da ’ya’ya shida a Kano kujerar Aikin Hajjin bana.

Fitaccen lauyan nan ɗan asalin jihar Kano kuma mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Barista Abba Hikima Fagge, ne ya sanar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata.

Ya ce, “Haj. Bilkisu Suleiman Fema wadda aka fi sani da Zinariyar Arewa, ta biya wa Mal. Haruna Bashir kujerar aikin Hajji, ta aika min da N200K a yi masa fasfo kuma ta yi alkawarin ba shi guzuri.

“Allah Ya saka mata da mafificin alheri. Amin. Wannan abu ya yi matukar faranta min wallahi,” kamar yadda ya wallafa.

Ya kuma ce tuni suka ƙaddamar da gidauniyar tallafa wa magidancin kuma har yanzu suna ci gaba da tattara masa gudunmawar.

A ranar Asabar ne dai wasu mahara suka shiga gidan inda suka hallaka mutanen ta hanyar yi musu kisan gilla.

Tuni dai ’yan sanda suka kama mutum uku da ake zargi, ciki har da ɗan uwan marigayiyar mai suna Umar Auwalu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *