Shugaban NAHCON Ya Kammala Ziyarar Aiki Ta Biyu A Shirye-shiryen Aikin Hajjin Bana

[ad_1]

Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya kammala ziyarar aiki ta biyu kafin fara jigilar maniyyata zuwa Aikin Hajji a kasar Saudiyya, wanda hakan ke wakiltar wani muhimmin ci gaba a shirye-shiryen Nijeriya na Aikin Hajji na 2026.

Ziyarar, wadda ta gudana daga 4 ga Janairu zuwa 19 ga Janairu, 2026, an yi ta ne da nufin inganta shirye-shiryen aikin, ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin Saudiyya, da kuma daidaita tsare-tsare don tabbatar da bin ƙa’idojin da Saudiyya ta gindaya domin gudanar da aikin hajjin da ke tafe lami lafiya.

  • Zargin Sace Masu Ibada Fiye Da 100 A Kaduna Ba Gaskiya Ba Ne – ‘Yansanda
  • Sojoji Sun Kashe Shugaban ‘Yan Ta’adda Munzir, Sun Kama Wasu 34 A Borno

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ahmad Muazu, Mataimaki kan al’amuran yada labarai ga Shugaban NAHCON ya fitar a ranar Talata.

A cewar sanarwar, tawagar NAHCON ta gudanar da wasu manyan tarurruka da manyan cibiyoyin Saudiyya, ciki har da Ma’aikatar Hajji da Umrah, Hukumar Kula da Jiragen Sama ta kasar (GACA), Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya, masu samar da ayyukan Mashāʾir, kamfanonin dake kula da bangaren masaukai da ciyarwa, kamfanonin jiragen sama, da kuma masu ruwa da tsaki na Nijeriya da ke Masarautar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *