’Yan bindiga sun kashe mutum 11 a ƙauyen Zamfara

[ad_1]



Aƙalla mutum 11 ne suka rasu bayan ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Ware da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce maharan sun shiga ƙauyen ne a ranar Alhamis, inda suka fara harbe-harbe kan mazauna yankin.

Ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar yankin, Amiru Ahmad Keta, ya ce an kai gawarwakin waɗanda suka rasu ƙauyen Keta domin yi musu jana’iza.

Ya ƙara da cewa mutanen da ke ƙoƙarin kwashe sauran gawarwakin sun ja da baya saboda maharan sun kore su.

A cewarsa har yanzu ba a san ainihin adadin waɗanda aka kashe ba.

Haka kuma jami’an tsaro ba su kai ɗauki ƙauyen ba.

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da yawaitar hare-haren ’yan bindiga.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *