Kwankwaso Bai Taɓa Neman Kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa Ba – NNPP
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta ƙaryata rahotannin da ke cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya nemi kujerar mataimakin shugaban ƙasa a matsayin sharaɗin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Jam’iyyar ta ce labaran ƙarya ne da aka ƙirƙira domin ɓata sunan tsohon gwamnan Jihar Kano.
- Tsaro: An Sake Buɗe Kwalejin Jihar Kwara Bayan Rufeta A Baya
- 2027: Atiku Ya Yi Ganawar Sirri Da Shugabannin Jam’iyyar ADP Kan Jita-Jitar Takarar Obi Da Kwankwaso
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar na Ƙasa, Ladipo Johnson, ya fitar, ya ce Kwankwaso bai taɓa shirin barin NNPP ya koma APC ba, kuma bai taɓa yin wata tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu ko wakilansa kan sauya sheƙa ba.
“Maganar cewa Kwankwaso ya nemi kujerar mataimakin shugaban ƙasa domin ya koma APC ƙarya ce,” in ji Johnson.
“Bai taɓa tunanin barin NNPP ya koma APC ba.”
Johnson ya ce ganawar ƙarshe tsakanin Kwankwaso da Shugaba Tinubu ta gudana ne a watan Janairun 2024, kuma babu wata tattaunawa kan komawa APC.
“Ganawarsa ta ƙarshe da Shugaban Ƙasa ta kasance a Janairun 2024, kuma babu wata magana ko kaɗan kan sauya sheƙa zuwa APC,” ya ce.
Kakakin NNPP ya ƙara da cewa waɗanda ke yaɗa waɗannan jita-jita wataƙila su ne suka yi niyyar komawa APC kuma yanzu sun koma.
“Waɗanda ke yaɗa waɗannan labarai, mai yiwuwa su ne suka yi shirin komawa APC kuma yanzu sun aiwatar da hakan,” in ji shi.
Ya zargi wasu daga cikin manyan ‘yan siyasa da ɗaukar nauyin ƙirƙirar labaran ƙarya domin ɓata Kwankwaso da siyasarsa.
“Wannan shiri ne na ɓata masa suna da kuma hana kafa ƙawance mai ƙarfi da zai iya ƙalubalantar tsarin mulki na yanzu,” in ji Johnson.
Jam’iyyar ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da waɗannan rahotanni, tana jaddada cewa Kwankwaso na ci gaba da mayar da hankali wajen yi wa jama’a hidima.
“Muna kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da waɗannan labaran na yaudara,” in ji shi.