’Yan siyasa su daina amfani da matasa wajen tayar da tarzoma — Uba Sani
[ad_1]
Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya gargaɗi ’yan siyasa da su daina tayar da tarzoma ko amfani da matasa wajen rikice-rikicen siyasa, yana mai jaddada cewa doka za ta kama duk wanda aka samu da hannu a haddasa rashin zaman lafiya, komai girman matsayinsa.
Gwamnan ya yi wannan gargaɗi ne yayin da yake jawabi a wani taro da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Kubau ta jihar.
A cewarsa, gwamnatinsa na ci gaba da wayar da kan al’ummar jihar da su zauna lafiya tare da yin hattara da masu yunƙurin jawo fitina a cikin al’umma.
“Duk wanda ya ce ku je ku tayar da fitina, ku ce masa ya tura yaronsa ya je ya yi harkar siyasa,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa bai dace ’yan siyasa su rika amfani da matasan jama’a wajen cimma muradunsu ba, yana mai cewa duk wanda ke son shiga siyasa ya fito da ’ya’yansa su shiga a fili.
“Kowane ɗan siyasa yana da ’ya’ya. Su fito da su su je su yi harkar siyasa a titi, kada su saka ku. Domin doka ba ta san kowa ba, kuma ba ta fifita wani,” in ji shi.
Gwamna Uba Sani ya kuma yi kira ga matasan jihar da su guji bari a yi amfani da su wajen rikicin siyasa, yana mai jaddada cewa zaman lafiya shi ne tubalin ci gaban Jihar Kaduna.
“Kada ku yarda a yi amfani da ku a rikicin siyasa. Ku ci gaba da zama lafiya a Kaduna. AlhamdulilLahi, muna cikin zaman lafiya a wannan jihar,” in ji gwamnan.
Ya sake nanata cewa duk wanda ya haddasa rashin zaman lafiya a Kaduna, doka ba za ta saurara masa ba.
“Komai girman mutumin da ya kawo rashin zaman lafiya a Kaduna, doka sai ta kama shi. Na faɗa muku wannan, ko wanene shi,” in ji shi.
Gwamnan ya kammala da kira ga al’ummar jihar da su zauna lafiya tare da kauce wa duk wani abu da zai haifar da rarrabuwar kawuna bisa addini ko kabilanci.
“Babu bambancin addini ko ƙabila. Allah ne Ya halicce mu duka, kuma Kaduna ita ce jiharmu. Saboda haka, mu zauna lafiya,” in ji gwamnan.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link