’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno

[ad_1]



Rahotanni sun tabbatar da rasuwar wasu sojoji huɗu, bayan ’yan ta’adda sun kai hari yankin Ngamdu na Jihar Borno.

Jihar Borno ta daɗe tana fama da hare-haren ta’addanci, musamman daga ƙungiyar Boko Haram.

Ko da yake wasu mazauna yankin sun ce sojoji 10 ne suka mutu, sai dai mai magana da yawun rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, bai tabbatar da hakan ba cikin sanarwar ya fitar a ranar Juma’a.

Amma rahotanni sun bayyana cewa sojoji huɗu ne suka mutu, yayin da wasu biyar suka jikkata a yayin harin.

A cewar Kanar Sani, ’yan ta’addan sun yi amfani da roka, jirage marasa matuƙa, da bama-bamai wajen kai harin.

Sai dai sojojin sun mayar da martani, inda suka kashe da dama daga cikin ’yan ta’addan.

Ya ƙara da cewa wasu motocin yaƙi na sojojin sun lalace, amma duk da haka dakarun sun yi tsayin daka wajen yaƙar maharan.

Bayan harin, ’yan ta’addan sun yi ƙoƙarin hana bin hanyar Ngamdu zuwa Damaturu, wanda hakan ya tilasta rufe hanyar na ɗan lokaci.

Daga baya,sojoji sun cire bama-bamai guda uku, sannan suka sake buɗe hanyar ga matafiya.

Laftanar Kanar Uba, ya ce an ƙara wa dakarun kayan yaƙi da harsasai domin ci gaba da fafatawa.

Rahotanni sun nuna cewa gawarwakin ’yan ta’adda kusan 15 aka samu a kusa da ƙauyen Bula Wura.

Rundunar Sojin Najeriya ta yaba wa jarumtar dakarun, tare da tabbatar wa jama’a cewa zaman lafiya ya samu a yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *