Dan majalisar Zamfara ya sha mari da ruwan duwatsu a wajen ’yan mazaɓarsa

[ad_1]



Dan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar karamar hukumar Maru ta Kudu, Hon. Mika’ilu Kabiru Dangulbi, ya sha duka tare da ruwan duwatsu a garin Dansadau na jihar.

Lamarin ya faru ne lokacin da ya raka tawagar Gwamna Dauda Lawal zuwa masarautar Dansadau domin ziyara.

Al’ummar yankin sun nuna rashin jin daɗi da shi tun bayan nasarar da ya samu a zaben 2023, inda suka ce ya zauna a Gusau maimakon ya zauna tare da su duk da matsanancin halin tsaro da suke ciki sakamakon ta’asar ’yan fashin daji.

Yankin Dansadau na daga cikin wuraren da suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga a jihar Zamfara.

A lokacin tashin hankali, matasan sun yi ta dukan danmajalisar, wasu na cewa “ku ji masa rauni”.

Jami’an tsaro sun yi ta ƙoƙarin tsare shi da shigar da shi mota domin kubutar da shi, sai dai hakan ya yi wuya saboda cunkoson jama’a. Daga bisani jami’an tsaro suka samu nasarar fitar da shi daga wurin.

An bayyana cewa Hon. Dangulbi ya samu kujerar majalisa ne da goyon bayan al’ummar yankin, amma daga baya suka zarge shi da yin biris da su.

Jaridar Aminiya ta yi hira da Malama Sallame, mazauniyar Dansadau wadda ke yin tafiye-tafiye zuwa Gusau duk da haɗarin hanya.

Ta ce hanyar Gusau zuwa Dansadau ta lalace ƙwarai, duk da cewa Gwamna Dauda Lawal ya bayar da kwangilar gyaranta a bara.

Sai dai ta ce aikin yana tafiyar hawainiya, inda daga cikin kilomita 100 da aka tsara, ba a kammala ko kilomita 20 ba.

“Aikin hanyar kamar ba a fara ba. Hanyar Dansadau tamkar hanyar mutuwa ce. Na sha ganin mutane suna faɗuwa daga mota, babu mai taimaka musu. Wasu su mutu, wasu su tsira. A makon da ya gabata na kirga gawarwaki uku a gefen hanya daga Dansadau zuwa Gusau,” in ji Sallame.

Ta ƙara da cewa al’ummar yankin na cikin mawuyacin hali, musamman a kauyukan Dandalla, Dangulbi, Dankurmi, Gobirawar Chali, Madada, Kallale, Sangeku da sauransu.

Ana ganin fushin da al’ummar suka nuna ga Hon. Dangulbi ya samo asali ne daga rashin aiwatar da ayyuka da kuma kin kula da matsalolin tsaro da suka addabi yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *