’Yan sanda sun haramta amfani da ‘knockout’ a Kaduna

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta sanar da haramta amfani da knockouts da kayan wasan wuta a duk fadin jihar, sakamakon ƙalubalen tsaro da kuma kare lafiyar al’umma.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, DSP Mansir Hassan, ya fitar a ranar Laraba, ya ce an dauki wannan mataki ne domin hana ’yan daba da masu aikata laifuka amfani da karar fashewa wajen tayar da hankula ko aikata ayyukan ta’addanci.

Sanarwar ta ce: “Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta haramta amfani da knockouts da kayan wasan wuta a duk fadin jihar bisa dalilan tsaro da kare lafiyar al’umma.”

Rundunar ta shawarci mazauna jihar da su gudanar da bukukuwansu cikin natsuwa tare da bin umarnin, inda ta jaddada cewa amfani da knockouts da fireworks yanzu “haramun ne gaba ɗaya” a duk fadin jihar.

A cewar rundunar, an dauki wannan mataki ne bayan samun sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa wasu bata-gari sun fara amfani da knockout a wasu yankuna, lamarin da ke tayar da hankalin jama’a tare da jefa tsoro a cikin al’umma.

Sanarwar ta kara da cewa: “Rundunar ta samu sahihan bayanan sirri daga majiyoyi daban-daban cewa wasu bata-gari sun fara amfani da knockouts, wanda hakan ke damun mazauna yankuna tare da haddasa tsoro da firgici.”

’Yan sanda sun yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana amfani da ko yana da hannu wajen amfani da knockouts, za a kama shi tare da hukunta shi bisa doka.

Daga nan sai rundunar ta bukaci mazauna jihar da su hada kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka a jihar.

Rundunar ’Yan Sandan ta sake jaddada kudurinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kiran jama’a da su rika kai rahoton duk wanda ya karya wannan doka zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *