Jiragen sama a faɗin duniya sun dakatar da zirga-zirga zuwa Gabas ta Tsakiya
[ad_1]
Wasu manyan kamfanonin jiragen sama na duniya sun fara dakatar da zirga-zirgarsu zuwa ƙasashen Gabas ta Tsakiya, sakamakon tashin hankalin da ke ƙara ƙamari a yankin.
Kamfanin Air France ya sanar da soke dukkan jiragen da ke zuwa da komawa Tel Aviv a Isra’ila da Beirut a Lebanon a ranar Asabar.
Iberia Express, mallakin rukunin kamfanonin Iberia, ya soke jirgin da zai tashi zuwa Tel Aviv da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Asabar.
Kamfanin jiragen sama na Indiya, IndiGo, ya ce yana bibiyar yadda al’amura ke gudana a yankin, sai dai bai sanar da soke wani jirgi kai tsaye ba.
Japan Airlines ya soke jirgin da zai tashi daga Tokyo Haneda zuwa Doha a ranar Asabar, tare da soke jirgin da aka tsara cewa zai dawo a ranar 1 ga Maris.
Kamfanin LOT Polish Airlines ya mayar da jirginsa LO121 da ya taso daga Warsaw zuwa Dubai, inda ya koma Warsaw yana tsakiyar tafiya.
Kamfanin Lufthansa na Jamus ya dakatar da zirga-zirga zuwa da dawowa daga Tel Aviv, Beirut da Oman har zuwa ranar 7 ga Maris, sannan ya soke jiragen Dubai a Asabar da Lahadi. Haka kuma ya sanar da kauce wa sararin samaniyar Isra’ila, Lebanon, Jordan, Iraƙi da Iran zuwa ranar 7 ga Maris.
Norwegian Air ya dakatar da dukkan jiragen da ke zuwa da komawa Dubai a ranar Asabar, inda ya ce ba zai shafi Tel Aviv da Beirut ba, kasancewar zirga-zirga zuwa can kan fara ne a lokacin bazara.
Kamfanin Turkish Airlines ya soke jiragen Asabar zuwa Qatar, Kuwait, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Oman, tare da dakatar da dukkan jiragen zuwa Lebanon, Syria, Iraƙi, Iran da Jordan har zuwa ranar 2 ga Maris.
Virgin Atlantic ya ce zai kauce wa sararin samaniyar Iraƙi, lamarin da ya haifar da sauya hanyoyin wasu jirage, tare da soke jirgin VS400 daga London Heathrow zuwa Dubai a ranar Asabar.
Kamfanin Qatar Airways kuma ya sanar da dakatar da dukkan zirga-zirgar zuwa da dawowa daga Doha na ɗan lokaci, sakamakon rufe sararin samaniyar ƙasar Qatar.
A safiyar wannan Asabar ce Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran, wanda Shugaba Donald Trump ya bayyana a matsayin “babban aiki” sannan ya yi kira ga gwamnatin Iran ta watsar da makamanta.
Tuni dai ita ma Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya game da hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai mata da safiyar yau.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila, IDF ta fitar, ta tabbatar da gano makamai masu linzami da Iran ta harba cikin ƙasar, amma tana ƙoƙarin ganin ta kakkaɓo su.
Haka ma Qatar ta tabbatar da cewa Iran ta kai hari kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke ƙasar, kodayake ta ce an kakkaɓo hare-haren.
Ita ma ƙasar Bahrain ta tabbatar da kai hari kan sansanonin sojin ruwan Amurka da ke ƙasar, kodayake ba ta alaƙanta harin da kowace ƙasa ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link