Gwamna Dauda Ya Yaba Da Yadda Aiki Ke Tafiya A Babban Filin Wasa Na Gusau


Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya duba aikin sake fasalin filin wasa na Sardauna Memorial Stadium da ke Gusau, inda ya bayyana gamsuwarsa da inganci da kuma saurin aikin da ake yi.

Ya ce wannan aikin na nuna jajircewar gwamnatinsa wajen sabunta kayayyakin more rayuwa a jihar.

  • Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Abdulkadir Ibrahim A Matsayin Sabon Sarkin Katsinan Gusau Na 16
  • Jami’ar Gwamnatin Tarayya Da Ke Gusau Ta Yi Sabon Shugaba, Farfesa Tukur Adamu.

Gwamnan ya samu rakiyar babban sakatare na Ma’aikatar Ayyuka da Kayayyakin More Rayuwa, Injiniya Haruna Dikko Gusau, tare da sauran manyan jami’an gwamnati.

Sai dai Lawal ya jaddada muhimmancin ci gaba da wannan hanzari tare da kiyaye ingantattun ƙa’idojin gini domin tabbatar da kammala aikin a kan lokaci.

Sake fasalin filin wasan ya haɗa da inganta babban filin wasa, kujerun Ƴan kallo, ƙara yawan kujeru, tsarin magudanar ruwa, hanyoyin shiga na cikin filin, da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa domin mayar da filin wasan ya zama na zamani wanda ya dace da martabar jihar.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *