Gabas ta Tsakiya: Sufeto-Janar ya ba da umarnin sanya ido a Arewa
[ad_1]
Muƙaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Disu, ya umarci kwamishinonin ’yan sanda a faɗin Najeriya su sanya ido a yankunan Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, an ce umarnin ya shafi rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran.
An kuma buƙaci jami’an su tattara bayanan sirri, su yi aiki tare da shugabannin gargajiya da na addini, tare da ƙara sintiri a wuraren ibada da wuraren tarukan jama’a.
Umarnin ya zo ne bayan ’yan Shi’a sun yi zanga-zangar lumana domin jimamin rasuwar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Disu, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar na cikin kwanciyar hankali, tare da gargaɗin cewa duk wanda ya yi ƙoƙarin tayar da rikici zai fuskanci hukunci.
Ya kuma buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu tare da kai rahoton duk wani abu ga ’yan sanda.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link