Magoya bayan Gwamnan Kano sun ɗauki hankalin taron gangamin APC

[ad_1]



Masu goyon bayan Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf sun ɗauki hankalin jama’a da mamaye babban filin taron gangamin jam’iyyar APC da ke gudana a dandalin Eagle Square a Abuja.

Magoyan bayan, waɗanda akasarinsu matasa ne maza da mata, sun yi ta rera waƙoƙi da raye-raye ɗauke da taken goyon bayan takarar Gwamnan a zango na biyu, da kuma ta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Wakilan taron da ke ta kwarara zuwa wurin, sun tsaya suna kallon ɗaruruwan masu goyon bayan cikin sha’awa yayin da suke ta kai-komo daga wannan ɓangare zuwa wancan a wajen filin taron, inda sauran mutanen da ba su samu damar shiga ciki ba suka taru.

Yayin da yake zantawa da wakilin Aminiyaɗaya daga cikin tawagar mai suna Bello Gaya, ya bayyana cewa sun bar babban birnin jihar Kano ne da misalin ƙarfe 11 na daren Alhamis, inda suka isa filin taron da misalin ƙarfe 6 na safe ranar Juma’a, kuma sun kasance a wurin tsawon yini.

Daga baya da yamma, an fara ganin wasu masu goyon bayan daga wasu jihohin kaɗan-kaɗan suna isa wurin taron.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *