NNPC ya rage farashin man fetur a Legas da Abuja
[ad_1]
Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC) ya rage farashin litar man fetur a gidajen mansa zuwa N1,130 a birnin Legas, da kuma N1,165 a Abuja.
Wannan sabon farashin ya nuna ragi na N100 daga tsohon farashin da ake sayarwa N1,230 a Legas, sannan an samu ragin N95 daga N1,260 da ake sayarwa a Abuja.
Bincike ya nuna cewa tuni aka fara sayar da man a kan sabon farashin a gidajen man NNPC da dama a Legas, ciki har da waɗanda ke kan hanyar Isheri Oshun, Apple Junction, da Ago Palace Way.
Haka zalika, wasu gidajen man na kamfanin na ƙasa da ke Babban Birnin Tarayya sun fara sayar da man fetur ɗin a kan N1,165 kowace lita, ciki har da gidajen man da ke yankunan Jabi, Lifecamp, Wuse Zone 5, da Wuse Zone 4.
Wannan sabon farashin ya biyo bayan ragin da matatar man Dangote ta yi kwanan nan, inda ta rage nata farashin zuwa N1,075 a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai ke faɗuwa a kasuwar duniya.
A cewar shafin OilPrice.comfarashin ɗanyen mai na Brent ya faɗi warwas a ranar Talata da kusan kashi 27 cikin 100, inda ya sauka daga $119 a kowace ganga zuwa kusan $87.
Haka kuma, farashin man dizal yanzu ya koma N1,430 kowace lita, wanda ke nuna ragin N190 daga tsohon farashin sa na N1,620.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link