Idan Ana Fatan Cimma Nasara A Matakin Kasa Da Kasa, Wajibi Ne A Zabi Kasar Sin

[ad_1]

A Juma’ar nan ne aka rufe taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na nahiyar Asiya na Boao na shekarar 2026. Taron da ya mayar da hankali kan tattauna sabbin yanayi, da sabbin damammaki, da sabbin matakan hadin gwiwa, wanda kuma hakan ya ja hankalin masu zuba jari na duniya baki daya. Kazalika, batun shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15, da gina tashar cinikayya marar shinge ta Hainan, suka kasance kan gaba cikin muhimman batutuwan da aka tattaunawa tsakanin masu juba jari na ketare.

Denis Depoux, daya daga shugabannin cibiyar bincike da bayar da shawarwari ta Roland Berger, ya ce shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15, ya samar wa kamfanoni da wani yanayi na hasashe, tare da ba su zarafin gane inda aka dosa dangane da ci gaba a lokuta dake tafe, wanda hakan ya ba su ikon tsara manufofi domin gaba. Ga misali, shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 da Sin ta fara aiwatarwa, ya dora fifiko kan cin gajiyar sabbin makamashi, wanda hakan ke nufin tarin kamfanoni masu zaman kansu za su shiga a dama da su, kana za a shigar da tarin ma’aikata masu basira da kudaden gudanarwa. A cewar Denis Depoux, sun himmatu matuka wajen shiga hada-hada a babbar kasuwar kasar Sin. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *