Jirgi Marar Matuki Na Dakon Kaya Samfurin Changying-8 Ya Yi Nasarar Tashi A Karon Farko

[ad_1]

A yau Talata ne jirgi marar matuki na dakon kaya samfurin Changying-8 (NORINCO LUCA), ya yi nasarar tashi a karon farko, daga filin jirgin sama na Shangjie dake birnin Zhengzhou na kasar Sin, inda ya zama jirgi marar matuki na dakon kaya mafi girma da aka taba kerawa a duniya.

Jirgin Changying-8 ya yi tafiyar kusan mintuna 30, sannan ya sauka lami lafiya a filin, a wani mataki na kammala aikin tashinsa karon farko cikin nasara. An yi amfani da tsarin jagoranci na fasahar zamani, da tsarin sa ido bisa karfin bil’adama, kuma dukkan sassan jirgin sun yi aiki yadda ya kamata. Wannan ya nuna cewa kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba, a fagen jigilar kaya masu nauyin ton 3.5 ta amfani da jirgi marar matuki.

A halin yanzu, tattalin arzikin sararin sama kusa da doron kasa na kasar Sin, yana kara habaka zuwa ainihin ayyukan da ake gudanarwa. Nasarar tashin farko da jirgin Changying-8 ya yi, za ta gaggauta samun takardar izinin shiga kasuwa, da samar da jirgin bisa rukuni-rukuni, da kuma gudanar da ayyukan kasuwanci, tare da samar da ingantacciyar hanya mai aminci, da hikimar jigilar kaya ta sararin sama kusa da doron kasa. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *