’Yan bindiga sun kai sabon hari bayan kashe masu bikin aure a Kaduna

[ad_1]



Rahotanni daga Jihar Kaduna na cewa ’yan bindiga sun kaddamar da sabon hari a kauyen Kahir da ke Karamar Hukumar Kagarko, inda suke harbi kan mai uwa da wabi.

Kawo yanzu dai babu wani karin bayani game da harin ko halin da mutane suke ciki bayan harin na ranar Talata.

Wannan harin na zuwa ne bayan a ranar Lahadi da dare, ’yan bindiga sun bude wa mahalarta bikin aure wuta a kauyen, inda suka kashe akalla mutum 12, tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Aminiya ta ruwaito cewa maharan sun kuma jikkata mutane da dama, inda aka garzaya da su Babban Asibitin Kagarko, wasu mutum biyu da ke cikin mawuyacin hali kuma aka wuce da su Kaduna domin kula da lafiyarsu.

Hukumar ’yan sanda ta tabbatar da harin na baya, ba tar da bayar da alkaluman wadanda abin ya shafa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *