Amincewa Da Lamunin Dala Biliyan 6 cikin Sa’o’i 4: Atiku ya caccaki Tinubu da Majalisar Dattawa
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma jigo a jam’iyyar adawa ta ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan rahotannin da ke cewa majalisa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na amso wani sabon lamunin waje na dala biliyan 6 cikin wani dan gajeren lokaci—inda aka ce bai wuce sa’o’i huɗu ba bayan gabatar da kudurin.
A cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman kan Hulɗa da Jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Talata, Atiku ya bayyana wannan lamari ba kawai abin damuwa ba ne, har ma abin firgici ga duk ‘yan kasa masu kishi.
Ya lura cewa, yanke shawara mai irin wannan nauyi ga ƙasa, wacce za ta ƙara ɗora wa tattalin arziƙin da tuni yake cikin mawuyacin hali nauyi, tare da jingina makomar ‘yan baya, bai kamata a yanke wannan shawara cikin gaggawa ba.