Jami’an Tsaro Sun Ƙwace Fasfon El-Rufai A Filin Jirgin Saman Abuja – Hadimi
[ad_1]
Rahotanni sun nuna cewae jami’an tsaro sun yi yunƙurin kama tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a ranar Alhamis a Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ne, ya bayyana hakan ta shafukan sada zumunta.
- Sauya Sheka: Jigo A APC Ya Bukaci Shugabanin Jam’iyyar Su Yi Taka-tsan-tsan
- Gwamnatin Kano Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Hana Kwankwaso Shigowa Kano — Buba Galadima
Ya ce El-Rufai ya dawo daga birnin Cairo na ƙasar Masar lokacin da jami’an tsaro suka tare shi a filin jirgin saman.
A cewarsa, jami’an sun nemi ya bi su, amma El-Rufai ya ƙi amincewa, inda ya bayyana cewa ba zai bi su ba sai sun nuna masa takardar gayyata a hukumance.
Adekeye, ya kuma yi zargin cewa jami’an tsaron sun ƙwace fasfon El-Rufai daga hannun ɗaya daga cikin mataimakansa yayin da ake tsaka da kai ruwa rana.
Har yanzu ba a san wace hukuma ce jami’an tsaronta ke da hannu a lamarin.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa a baya-bayan nan, El-Rufai ya ce ana dab da kama shi.
Ya kuma yi zargin cewa ana matsa wa wasu ‘yan siyasa lamba su koma jam’iyyar APC.
El-Rufai dai ɗan siyasa ne da ke jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC).
[ad_2]
Source link