Ga Yadda Shugaban Uruguay Ya Takaita Ziyarar Aikinsa A Sin Da Kalma Daya
[ad_1]
Shugaban Uruguay Yamandú Orsi da tawagarsa sun isa filin jirgin sama na kasa da kasa na birnin Beijing dake kasar Sin da safiyar ranar 1 ga watan Fabrairu, daga bisani suka fara ziyarar aiki ta mako guda a Sin.
A ranar 6 ga watan, shugaba Orsi ya yi hira da wani shiri na tattaunawa da shugabanni mai suna “Leaders Talk” da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya gabatar a birnin Beijing, A lokacin hirar, yayin da aka tambaye shi kalmar da zai yi amfani da ita don takaita ziyararsa a Sin, Orsi ya ambaci “Godiya” da “Gaskiya”. Ya ce kalma ta farko da ta zo a kwakwalwarsa ita ce “Godiya”. Idan ya waiwayi abin da ya faru a baya da kuma abin da ya faru a yanzu, ya yi imanin cewa Sin tana wakiltar “Gaskiya”. Duk da cewa wannan “Gaskiya” ta samo asali ce daga mafarki, yanzu yana jin cewa yana cikin wannan “Gaskiya” wanda ke da alaka da tarihi mai dubban shekaru.
Orsi ya kara da cewa, lokacin da mutane suka fahimci wannan gaskiyar, yana zama da sauki a gina muhimmin tushe na aminci, ta haka ne za a kulla alaka mafi karfi. Hoton da kasar Sin ta nuna a bayyane yake, a cikin tsarin duniya na yanzu, wannan ita ce babbar fa’ida. (Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link