Majalisar Dattawa za ta yi zaman gaggawa a ranar Talata
[ad_1]
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya umarci dukkanin Sanatoci su koma Majalisa domin zaman gaggawa a ranar Talata, 10 ga watan Fabrairu, 2026.
An kira wannan zama ne kwanaki kaɗan bayan Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da ƙudirin da ke neman a riƙa tura sakamakon zaɓe ta lantarki.
A wata sanarwa da Magatakardar Majalisar, Emmanuel Odo, ya fitar, an buƙaci dukkanin sanatoci su halarci zaman.
Za a fara zaman gaggawar da misalin ƙarfe 12 na ranar Talata.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link