Su Yiming Ya Lashe Lambar Yabo Ta Farko Ga Sin A Gasar MilanCortina A Wasan Tsallen Zamiyar Kankara
[ad_1]
Zakaran gasar Olympic mai kare kambunsa, Su Yiming, ya lashe wa kasar Sin lambar yabo ta farko a gasar wasannin lokacin hunturu ta MilanCortina a jiya Asabar, inda ya lashe tagulla a fafatawar da aka gwabza a bangaren maza a wasan zamiyar kankara da ake daka tsalle a ciki.
Bisa ci gaba da nuna jarumta a wannan wasa mai cike da kasada, Su mai shekaru 21 ya daidaita tsakanin cimma buri da iya sarrafa kansa bayan da ya farfado daga faduwar da ya yi a kokarin neman cancantar kaiwa ga wasan karshe
Da yake tsokaci, Su ya bayyana cewa, “Ina matukar alfahari da kaina saboda na iya jure matsin lamba mai tsanani kuma har na samu damar amfani da dabaruna yadda ya kamata. A karshe, yanzu ina da ko wane nau’i na lambar yabo.” Inda ya kara da cewa, “Ina matukar farin ciki da sanya launin tutar kasa, ga ni tsaye a nan wajen karba wa kasarmu lambar yabo ta farko.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link