Ma’aukatan lafiya sun tsunduma yajin aiki
[ad_1]
Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya (JOHESU) da Ƙungiyar Ƙwararru a Fannin Kiwon Lafiya sun fara yajin aiki a yau Asabar.
Ƙungiyoyin sun ce gazawar gwamnati wajen aiwatar da sabon tsarin albashin ma’aikatan lafiya na CONHESS da kuma rashin kawo ƙarshen matsalolin da suka jima suna ƙorafi a kansu ne musabbabin tafiya yajin aikin.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Shugaban JOHESU na Ƙasa, Kwamared Kabiru Ado Minjibir, ya sanayawa hannu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link