Yadda Ake Miyar Margi (Margi Special)
[ad_1]
Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai ci gaba da koya mana Miyar Margi (Margi special) ta ‘yan Barno da Yobe:
Miyar Margi wata shahararriyar miya ce daga yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman tsakanin mutanen Borno da Yobe. Ana amfani da kayan gargajiya da suka hada da gauta, kifi ko nama, daddawa da kayan miya.
Kayan da ake bukata:
Kifi mai nama ko naman rago, Ataruhu da tattasai, Barkono ja, Albasa, Daddawa, Gauta (baobab leabes),Yaji, gishiri da maggi, Manja ko man gyada.
Yadda ake hada miyar:
A wanke kifi ko naman da kyau, a nika attaruhu, tattasai, barkono ja da albasa a hade.
A zuba kifi ko naman a tukunya tare da dan ruwa, gishiri da maggi. A bar shi ya tafasa har ya fara laushi.
Sannan a zuba nikakken kayan miya a cikin tukunyar. A bar su su dahu har su gauraya da naman ko kifin. Sannan sai a zuba daddawa a cikin miya. A juya sosai sannan a bar shi ya tafasa na ‘yan mintuna.
Sai a wanke gauta sosai kafin a zuba a cikin miya. A bar miya ta dan yi kauri haka.
A zuba dan manja don ya kara wa miyar launi da dandano. Sai a rage mata wuta, a bar ta ta dahu a hankali.
Sai a dandana a ji komai yaji, idan ana bukatar kari sai a kara gishiri ko maggi idan akwai.
Bambancin “Margi Special”:
Wasu masu dafa abinci suna kara dan dankali ko karas domin kara wa miya kauri da kamshi.
Abin da ake ci da miyar:
Tuwon masara, Tuwon dawa, Tuwon shinkafa, da Burabusko.
[ad_2]
Source link