Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia

[ad_1]



Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce babu wani addini ko mabiyansa da ake yi wa kisan ƙare dangi a jiharsa ko a Najeriya baki ɗaya.

Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta shirya a Abuja kan kare haƙƙoƙin mutanen da aka tilasta musu barin gidajensu.

Gwamna Alia, wanda tsohon Faston Katolika ne, ya ce: “A Binuwai, babu wani kisan kare addini, ƙabilanci, launin fata, ƙasa ko jiha.

“Muna da wasu matsalolin tsaro, amma ba kisan addini ba ne. Ya kamata mutane su duba ma’anar kisan ƙare addini ta Majalisar Ɗinkin Duniya.”

Ya kuma ce babu wani jihadi da ake yi a kowane ɓangare na Najeriya, ko da yake ƙungiyoyin ’yan ta’adda kamar Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso Gabas, suna iƙirarin  jihadi.

“Babu wani jihadi a Najeriya,” in ji Alia.

“A matsayina na Fasto kuma gwamna, ni ne zan fara yin magana idan hakan na faruwa a jihata ko a wani ɓangare na ƙasar nan.”

Kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya.

Amurka ta taɓa sanya Najeriya a cikin jerin  “Ƙasashen Masu Matsala ta Musamman” saboda cin zarafin addini, amma gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargi.

Kiristoci da Musulmai duka sun sha wahala sakamakon rashin tsaro, fashi da makami, da kuma garkuwa da mutane.

Gwamna Alia, ya ce ya gana da ofishin jakadancin Amurka don bayyana yadda halin tsaro yake a Binuwai.

“Na bayyana cewa babu kisan ƙare addini a Najeriya, musamman a Binuwai. Ma’anar Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta dace da yanayin nan ba,” in ji shi.

Jihar Binuwai ta jima tana fuskantar matsalolin da suka shafi kisan jama’a da sace mutane.

Bayanai sun nuna cewa sama da mutum 800 sun mutu, yayin da aka sace kusan mutum 400 cikin shekaru biyu da suka gabata.

A watan Yuni, aƙalla mutum 100 ne suka mutu a hare-haren da ’yan ta’adda suka kai a Ƙaramar Hukumar Guma.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *