Ribadu Ya Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Amurka Kan Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla

[ad_1]


Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci.

Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza.

A farkon watan nan, Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Nijeriya, kuma ya buƙaci ‘yan majalisar dokokin ƙasar, ciki har da ɗan majalisa Riley Moore, su binciki lamarin.

Ko da yake Nijeriya ta ƙaryata iƙirarin, amma Amurka ta ci gaba da jadadda zargin kisan Kiristoci.

A ranar Talata, mawaƙiyar Amurka, Nicki Minaj a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi magana a kan zargin cin zarafin Kiristoci a Nijeriya.

Tawagar Nijeriya, wacce ta haɗa da manyan jami’ai kamar Bianca Ojukwu, Kayode Egbetokun, da Lateef Fagbemi, sun gana da Moore don bayyana ƙalubalen tsaro, yaƙi da ta’addanci, da kare al’ummar ƙasar.

Moore, ya ce tattaunawar “ta kasance ta gaskiya, kuma mai amfani” kuma ya jaddada cewa Amurka na son ganin an ɗauki matakai don kare Kiristoci daga tashin hankali da ta’addanci.

Hakazalika, ya nuna shirin yin aiki tare da Nijeriya wajen yaƙar ƙungiyoyi irin Boko Haram, ISWAP, da sauransu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *