Rahoton KPMG Ya Shaida Karfin Gwiwar Kamfanonin Kasa Da Kasa Game Da Bunkasar Tattalin Arzikin Sin A 2026
[ad_1]
Wani rahoton bincike na shekarar 2025 da kamfanin KPMG ya fitar a baya bayan nan, ya nuna yadda kaso 94 bisa dari na manyan kamfanonin kasa da kasa ke da karfin gwiwa game da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, lamarin da ya sa kamfanonin ke fatan kara zuba jari a kamfanoni daban daban na babban yankin kasar ta Sin.
Rahoton yanayin da kasar Sin ke ciki dangane da hada-hadar tattalin arziki, wanda kamfanin na KPMG ya fitar a jiya Laraba, ya ce kaso 75 bisa dari na irin wadannan kamfanoni na da shirin wanzarwa, ko kara yawan jarinsu a kamfanonin babban yankin Sin a shekarar dake tafe.
Har ila yau, kaso 60 bisa dari na masu bayyana ra’ayi dangane da batun, na cewa sun karkata hankulansu zuwa ga babban yankin kasar Sin domin bunkasa hada-hadarsu, daga fadada jari zuwa neman riba. Kazalika, kaso 83 bisa dari sun mayar da wasu bangarori na ayyukansu zuwa babban yankin na Sin, musamman na sarrafa hajoji, da tsarin rarraba su, da bincike da samar da ci gaba.
Hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa sun jaddada wannan matsaya. Inda yayin taron karawa juna sani game da shekarar 2026 na mujallar Caijing, babban wakilin asusun bayar da lamuni na IMF dake kasar Sin Marshall Mills, ya ce duk da yanyin tangal-tangal mai karfi da ake fuskanta, tattalin arzikin kasar Sin ya nuna matukar juriya.
Bugu da kari, wani rahoto da kamfanin Bloomberg ya wallafa a watan Afirilun bana, ya fayyace yadda kasar Sin ta cimma manyan nasarori a wannan shekara duk da dumbin kalubale, kuma daga takaddamar cinikayya tsakaninta da Amurka zuwa saurin bunkasar fasahohin AI, wanda hakan ke nuna cewa bai dace wani bangare ya raina kasar Sin ba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link