Sanata Shehu Sani Ya Buƙaci Al’ummar Kaduna Su Zaɓi Mutane Masu Mutunci A Zaɓen 2027
[ad_1]
Daga Shehu Yahaya Kaduna.
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bukaci al’ummar Jihar Kaduna da su yi tunani mai zurfi tare da natsuwa wajen zaɓar shugabanni nagari a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.
Sanata Shehu Sani ya ce lokaci ya yi da al’ummar jihar Kaduna za su bai wa gwamnatin Gwamna Uba Sani cikakken goyon baya, bisa la’akari da ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke aiwatarwa a fadin jihar.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 5 Da Ake Zargin ‘Yan Bindiga Ne A Kano.
- Sin Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Bunkasa Tsimin Makamashi Da Rage Fitar Da Hayakin Carbon
Ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakwancin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, a gidansa da ke Kaduna.
A cewarsa, al’ummar Kaduna ya kamata su yi hattara da tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i, musamman dangane da duk wani yunkuri da yake yi na tallata dan takara ta jam’iyyar ADC.
Sanata Shehu Sani ya tunatar da jama’a abubuwan da suka faru a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023, inda aka rushe gidaje tare da korar mutane da dama daga aikinsu. Ya ce a halin yanzu Allah ya albarkaci jihar Kaduna da gwamna mai tausayi, dattako da mutunta jama’a, wanda baya amfani da kafafen yada labarai wajen zagin mutane.
“Ba za mu koma gidan jiya ba,” in ji Sanatan. “Mutumin da ya yi barna shi ne yanzu yake yawo yana neman goyon bayan jama’a. Ku yi hattara kada ku bari a sake maimaita abin da ya faru.”
Ya kara da cewa Gwamna Uba Sani ya ware Naira miliyan 100 ga kowacce mazaba domin ayyukan ci gaba, tare da bukatar jama’a su tabbatar sun amfana da irin wadannan tsare-tsare na alheri.
Sanata Shehu Sani ya ce akwai yunkurin dawowar tsohon gwamna domin tsayar da wani gwamna a jihar Kaduna, inda ya gargadi al’umma da kada su bari hakan ya faru, domin kada a koma rushe gidaje da korar jama’a bisa wasu hujjoji.
A karshe, ya jaddada cewa Gwamna Uba Sani ya mutunta al’ummar Kaduna, don haka ya dace jama’a su biya wannan alheri ta hanyar hada kai da zabar mutane masu mutunci da nagarta, musamman ta hanyar goyon bayan jam’iyyar APC a zaben da ke tafe.
Ya ce zaben 2027 zai kasance zabe ne na makoma, inda al’ummar Kaduna za su zabi tsakanin ci gaba da komawa baya
[ad_2]
Source link