Mece Ce Aniyar Shugaban Amurka Game Da Kafa “Tawagar Zaman Lafiya”?

[ad_1]

A ’yan kwanakin nan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar White House ta Amurka, shugaban kasar Donald Trump ya ayyana kaddamar da wata kungiya, wadda ya yiwa lakabi da “Tawagar Zaman Lafiya ko “Board of Peace”, wadda za ta gudana a karkashin ikonsa, kuma wadda membobinta za su yiwa gidauniya ta zunzurutun kudi har dala biliyan daya.

A wannan gaba da labarin kaddamar da gidauniyar ke kara bazuwa, har ma wasu kasashe kalilan suka fara nuna amincewa da ita, a daya hannun shugaba Trump ya umarci a janye Amurka daga hukumomin kasa da kasa har 66, ya kuma sake sanar da ficewar kasar ta Amurka daga hukumar lafiya ta duniya WHO a hukumance.

Masharhanta na ganin idan har shugaban na Amurka zai dauki wannan mataki na janye kasarsa daga tarin hukumomin kasa da kasa a dan kankanen lokaci ba tare da wani dalili kwakkwara ba, to mene ne ma’anar kafa wata tafiya mai lakabin “Tawagar Zaman Lafiya”? Amsar hakan a bayyane take, shugaba Trump na yunkurin kara karkata manufofin waje na kasarsa ne zuwa tafarkin amfani da karfin fada-a-ji na bangare daya. Wanda ko shakka babu zai haifarwa Amurka karin kebe kanta maimakon bunkasa cudanya, da kara raba tafiyarta da sauran sassan kasa da kasa.

Ko da yake gwamnatin shugaba Trump na cewa, makasudin kafa wannan tafiya ta “Tawagar Zaman Lafiya ko “Board of Peace”, shi ne ingiza matakan wanzar da zaman lafiya, da sake gina wurare da yaki da daidaita ciki har da zirin Gaza, ta amfani da basirar dukkanin sassan kasa da kasa. A hannu guda masu ganin baiken manufar na ganin tafiyar za ta iya zama wata dabara ta baiwa Amurka damar sarrafa matakan da ya dace kasashen duniya su dauka dangane da batutuwan da suka shafe su baki daya.

Kaza lika, tafiyar za ta zamo tamkar kishiya ga majalisar dinkin duniya, don haka ne ma da yawa daga kasashen Turai suka kaurace mata. In ban da tsirarun kasashe da suka amsa gayyatar da shugaban na Amurka ya mika ta shiga tafiyar da ya kirkiro.

Kwararru da masu nazarin dangantakar kasashen duniya, na ganin burin Trump shi ne mallake ikon fada-a-ji, da tasirin hawan kujerar na ki shi kadai, ta yadda zai rika sarrafa akalar batutuwan kasa da kasa ba tare da raba iko da sauran sassa ba, kuma hakan tamkar komawa salon danniya ne, da mayar da duniya hannun Amurka ita kadai. Matakin da ko alama sassan kasa da kasa ba za su taba lamunta ba! (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *