Yaƙin Amurka/Israila Da Iran: Gabas Ta Tsakiya Na Tsaka-mai-Wuya

[ad_1]

A ranar Asabar da ta gabata ne, aka kashe jagoran juyin-juya-halin musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya mayar da ƙasar a matsayin mai tsananin adawa da Amurka tare da faɗaɗa ikonta na soji a yankin gabas ta tsakiya a hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kamar yadda wani babban jami’in Isra’ila ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a yammacin ranar.

Amurka da Isra’ila sun kai hare-haren soji ne a kan ƙasar ta Iran, inda suka kashe manyan shugabanninta.

Shugaba Amurka Donald Trump ya ce, waɗannan hare-hare ko shakka babu za su kawo ƙarshen barazanar tsaro ga Amurka tare da bai wa Iraniyawa damar hamɓarar da waɗannan shugabanni nasu.

  • Kasar Sin Za Ta Yi Aiki Da Sauran Kasashe Wajen Karfafa Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya
  • Arewa Maso Gabashin Jigawa: Abokan Babandede Sun Dauki Harama

Jim kaɗan bayan faruwar al’amarin, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce; akwai alamun da ke nuna cewa, Khamenei ya “mutu”, bayan harin da Amurka da Isra’ilan suka kai musu. Haka zalika, Shugaba Trump da Firayim Minista, Netanyahu sun ce; an nuna musu hoton gawarsa da aka ɗauko daga harabar da aka kai harin.

Hotunan tauraron Ɗan’adam a baya, sun nuna ɓarnar da harin ya yi a harabar Khamenei a Tehran a cewar BBC.

Khamenei, mai shekaru 86, ya zama jagoran juyin-juya-halin musulunci na Iran a shekarar 1989, bayan mutuwar wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci, Ayatollah Ruhollah Khomeini.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a matsayinsa na shugaban ƙoli, ya riƙe madafun iko kan harkokin siyasa, soja da kuma cibiyoyin addini na Iran da tsara manufofin cikin gida da kuma jagorantar hulɗar ƙasashen waje.

Isra’ila ta daɗe tana kallonsa a matsayin mai kawo tarzoma a yankin gabas ta tsakiya, saboda goyon bayansa ga ƙawancen da Hamas, Falasdinawa da kuma ƙungiyar Hizbullah ta Lebanon.

Lokacin da Isra’ila da Iran suka gwabza yaƙi na kwana 12 a watan Yunin 2025, Ministan Tsaron Isra’ila, Isra’ila Katz ya yi barazanar kashe shi, yana mai cewa; babban shugaban “ba zai iya ci gaba da wanzuwa a duniya ba.”

Hukumar leƙen asiri ta Amurka, ta yi hasashe a cikin makwanni biyu kafin kai harin cewa; idan aka kashe Khamenei, za a iya maye gurbinsa da wasu masu tsatsauran ra’ayi daga dakarun kare juyin, kamar yadda wasu majiyoyi biyu suka bayyana kan bayanan.

Nijeriya ta shiga sahun ƙasashen duniya, masu bayar da shawarar sasantawa, bayan Amurka da Isra’ila sun kai wa Iran ɗin hari.

A halin da ake ciki yanzu, ƙasashen duniya da shugabannin ƙasashen duniya sun buƙaci a sasanta bayan da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da wani gagarumin farmaki kan Iran a ranar Asabar, gwamnatin Najeriya ta bi sahun sauran ƙasashen da ke neman a dakatar da fafatawar.

Wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, Kimiebi Ebienfa ya fitar bayan ƙaddamar da harin, “Gwamnatin Nijeriya na fata tare da yin kira ga ɓangarorin da ke rikici da juna, da su kwantar da hankulansu ta hanyar komawa teburin tattaunawa, domin cimma muradun zaman lafiya da zaman tare a duniya.”

A wani labarin kuma a Amurka, shugaba Trump ya ce; an kai harin ne da nufin kawar da shirin nukiliyar Iran da kuma haifar da sauye-sauye a gwamnati, bayan da wasu da dama na tattaunawar nukiliyar da ɓangarorin biyu suka kasa cimma matsaya.

Har ila yau, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta buƙaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da ya ɗauki matakin gaggawa, domin fuskantar haƙƙin zaman lafiya da tsaro na ƙasa da ƙasa.

Ita ma da take mayar da nata martanin kan rikicin, Gwamnatin Birtaniyya ta ce; ba ta shiga cikin yaƙin ba, sannan kuma ba ta goyon bayan ganin ƙara ruruwa al’amarin zuwa wani babban rikici.

Ta ƙara da cewa, a baya-bayan nan ta ƙara inganta ƙarfinta na bayar da kariya a yankin gabas ta tsakiya, inda ta ƙara da cewa; abin da ta sa a gaba yanzu shi ne, kare lafiyar ‘yan Burtaniya a yankin.

“Bai kamata a taɓa barin Iran ta ƙera makamin Nukiliya ba, kuma shi ya sa muke ci gaba da goyon bayan ƙoƙarin da ake yi na cimma matsaya ta hanyar shawarwari,” in ji gwamnatin a cikin wata sanarwa.

A nata martanin, Gwamnatin Jamus ta bakin kakakinta a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce; Isra’ila ta sanar da Jamus tun da farko. Sanarwar ta ce, shugaba Friedrich Merz “yana sa ido sosai a kan ci gaban da ake samu, sannan kuma yana cikin haɗin gwiwa tare da abokan hulɗar Turai.”

An shirya cewa, Mista Merz zai gana da Mista Trump a Washington a mako mai zuwa.

A nasa ɓangaren, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi kira da a kawo ƙarshen hare-haren tare da neman a gudanar da taron kwamitin sulhu.

Har ila yau ya rubuta cewa, dole ne shugabannin Iran su fahimci cewa; a yanzu ba su da wani zaɓi da ya wuce shiga tattaunawa ta gaskiya a kan shirinsu na nukiliya, ya kuma ƙara da cewa; al’ummar Iran “dole ne su ma su iya gina tasu makomarsu a cikin ‘yanci.”

Daga Ostiraliya kuma, Firayim Minista Anthony Albanese, yana cikin ‘yan tsirarun shugabannin da ba su fito fili sun nemi a sasanta ba. Sanarwar ta ce; “Muna goyon bayan Amurka wajen hana Iran mallakar makamin nukiliya da kuma hana Iran ci gaba da barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya.” Ya ce, Iran ta kasance “mai tayar da hankali”, tsawon shekaru da dama, ya kuma ba da misali da hare-haren ta’addanci guda biyu na baya-bayan nan da aka kai a Australiya da gwamnatin ta ce; wani ɓangare ne na sojojin Iran ya jagoranta.

Firaministan Ƙasar Kanada, Mark Carney da ministan harkokin wajensa, Anita Anand sun goyi bayan matakin na Amurka. “Kanada tana goyon bayan matakin Amurka na hana Iran mallakar makamin nukiliya da kuma hana gwamnatinta ƙara yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya,” in ji sanarwar.

Daga Tarayyar Turai (EU) kuma, Kaja Kalas, babbar jami’ar diflomasiyya ta EU ta ce; ta yi magana da ministar harkokin wajen Isra’ila da sauran jami’ai a yankin, kuma tana “haɗa kai tare da abokan haɗin gwiwar Larabawa, domin gano hanyoyin diflomasiyya.” Babban jami’in zartarwa na EU, Ursula ɓon der Leyen, da babban shugabanta na siyasa, Antonio Costa, sun rubuta a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa cewa; yana da matuƙar muhimmanci a hana “duk wani mataki da zai iya haifar da tashin hankali ko lalata tsarin hana zaman lafiya a duniya.”

Firayim Ministan Spain Pedro Sánchez, ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai, ya kuma yi Allah wadai da gwamnatin Iran. “Ba za mu iya sake samun wani dogon yaƙi mai ɓarna a gabas ta tsakiya ba,” in ji shi.

Firayim Ministan Sweden, Ulf Kristersson, ya yi kira da a sasanta, amma kuma ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa ‘yan kasar ta Iran, a wani mataki na nuna adawa da zanga-zangar da aka yi a watan Janairu da gwamnati ta murƙushe ta. Ya ce, goyon bayan da Iran ke bai wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, ya daɗe yana taɓarɓara al’amura, kuma bai kamata a taɓa bari ta ƙera makaman ƙare dangi ba.

Haka zalika, a Ƙasar Labanon, manyan shugabannin, sun yi kira ga dukkan ɓangarorin da su ba da fifiko ga jin daɗin al’ummar Iran.

Kalaman dai, sun yi nuni ne ga ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon, a daidai lokacin da ake tantama kan ko ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran na iya yunƙurin shiga cikin rikicin, domin nuna goyon baya ga Iran.

A wani labarin kuma, hukumomi a Ƙasar Saudiyya, sun bayyana rahotannin harin ramuwar gayya da Iran ta kai, kan ƙasashen Larabawa da suka haɗa da Bahrain da Kuwait da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a matsayin cin zarafi a fili ga ɗaukacin ƙasarsu.

“Saudiyya ta tabbatar da cikakken goyon bayanta ga waɗannan ƙasashe ‘yan uwanta tare da yin alƙawarin taimaka musu a duk wani mataki da za su ɗauka,” in ji ma’aikatar harkokin wajen ƙasar a cikin wata sanarwa ta kafofin sada zumunta.

A Ƙasar Switzerland, gwamnatin ta ce; “ta damu matuƙa da kai wannan hari”. Ta yi kira da “cikakkiyar mutunta dokokin ƙasa da ƙasa”, tare da yin kira ga dukkan ɓangarorin, “su yi iya iyawarsu”, da kuma ƙare fararen hula.

Har wa yau, Firaministan Malaysiya Anwar Ibrahim, ya bayyana a kafar sada zumunta ta yanar gizo cewa; hare-haren sun kai yankin gabas ta tsakiya cikin tashin hankali. “Ina kira ga Amurka da Iran, da su bi tafarkin diflomasiyya maimakon ƙara ta’azzara lamarin, sannan kuma ƙasashen duniya su tabbata sun yi aiki cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba,” in ji shi.

A Ƙasar Indonesiya kuma, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta faɗa a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa; “ta yi matuƙar nadamar gazawar shawarwarin da aka yi tsakanin Amurka da Iran.”

Shugaban Indonesiya, Prabowo Subianto, a shirye yake ya tafi Tehran, don “samar da tattaunawa domin maido da ingantaccen yanayin tsaro,” in ji sanarwar.

Daga birnin Beijing, ma’aikatar harkokin wajen Ƙasar Sin, ta bayyana a shafukan sada zumunta cewa, Beijing ta damu matuƙa da wannan kai hari. Ma’aikatar ta ce, “Ya kamata a mutunta ikon ƙasar Iran, tsaro da kuma iyakokinta.”

Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi Allah-wadai da hare-haren, yana mai cewa; sun keta hurumin Ƙasar Iran tare da jefa al’ummarta cikin haɗari, koda-yake ya ce; harin ramuwar gayya da Iran ta kai kan ƙasashen yankin Gulf na Farisa, abu ne da ba za a amince da shi ba.

Shugaban Cuba, Miguel Díaz-Canel, ya yi Allah-wadai da hare-haren, yana mai kiransu da cewa; “rashin mutunta dokar ƙasa da ƙasa da kuma Yarjejeniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya.” Mista Díaz-Canel, ya faɗa a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa; “dole ne al’ummar duniya su ɗauki matakin gaggawa, domin dakatar da wannan ta’addanci.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *