’Yan sanda sun kama ɗan bindiga, sun ceto mutum 2 da aka sace a Nasarawa
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, ta ceto mutum biyu da aka sace tare da kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne a jihar.
Kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel, ya ce a ranar 3 ga watan Fabrairu, 2026, ’yan sanda sun ceto David O. daga Tudun Amba a Lafia.
David ya hau babur daga Lafia zuwa Assakio, amma direban babur ɗin ya sauya hanya zuwa cikin daji a ƙauyen Kireyi.
Wanda ake zargi ya tsere, kuma ’yan sanda na nemansa ruwa a jallo.
A wani labarin kuma, ’yan sanda sun kama Jamilu Salisu bisa zargin sace wani ɗalibi ɗan shekaru 14 a kusa da wani masallaci a Gitata.
An ceto yaron, amma wani abokin aikin nasa ya tsere.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya bayar da umarnin a tsananta neman waɗanda suka tsere domin gurfanar da su s kotu.
Ya kuma gode wa al’ummar jihar kan haɗin kai, inda ya sake tabbatar da ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaro a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link