Iran ta yi alƙawarin kai wa Isra’ila da Amurka munanan hare-hare
[ad_1]
Iran ta yi alƙawarin kai hare-hare munanan hare-hare domin mayar da martani ga farmakin da Israel da Amurka suka kai mata.
A ranar Asabar, an ji ƙarar fashe-fashe a wasu biranen Iran da suka haɗa da Kermanshah, Lorestan, Tabriz, Isfahan da Karaj.
Ministan tsaron Isra’ila ya ce ƙasar ta kai harin ne tun da wuri domin kawar da abin da ta kira barazana ga tsaron Isra’ila.
Wannan sabon farmaki ya biyo bayan yaƙin sama na kwanaki 12 da aka yi tsakanin Isra’ila da Iran a watan Yunin 2025.
Tun da farko Amurka da Isra’ila sun yi gargaɗi cewa za su sake kai hari idan Iran ta ci gaba da shirinta na ƙera makaman nukiliya da makamai masu linzami.
Wani jami’in Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ƙasar na shirin kai martani mai tsanani.
Rahotanni sun ce Jagoran ƙoli na Iran, Ali Khamenei, ba ya Tehran lokacin da makaman suka sauka, kuma an kai shi wani waje mai tsaro.
Shi ma Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce harin an kai shi ne domin kare muradun Amurka da kuma kawar da abin da ya kira barazanar daga Iran.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link