Yadda Ciwon ‘Glacoma’ Ke Haddasa Makanta
[ad_1]
Mutane da dama na kamuwa da cutar ‘Glacoma’ ba tare da sun sani ba, shi yasa yake da mutuƙar muhimmanci da zarar mutum ya ji wani abu da ke nuna alamun ciwon ido, ya yi maza ya garzaya zuwa asibiti.
Har ila yau, ‘glacoma’ wata cuta ce wadda take kama idanu, ta sa ganin mutum ya samu matsala, wanda hakan kan jawo makanta. Kazalika wannan cuta, mafi yawancin lokaci ta fi kama masu shekaru, waɗanda shekarunsu suka haura 40.
- Kasar Sin Ta Sanya Wasu Kamfanonin Japan Karkashin Kayyadewar Tsarin Sa Ido A Fannin Fitar Da Kayayyaki
- Hainan Ta Karbi Karin Masu Bude Ido Daga Ketare
Sannan, idan akwai masu wannan cuta a gidanku ko a danginku, akwai barazana ko yiwuwar kamuwa da ita. Don haka, da zarar ka fara yawan jin ƙaiƙayi wanda ba ka saba da jin sa ba, ko ciwon ido, ka yi maza ka garzaya zuwa asibiti.
Haka zalika, masu fama da hawan jini da kuma waɗanda suka jima suna shan sha-ka-fashe, su ma akwai barazana tare da yiwuwar kamuwa da wannan cuta a tare da su.
Haka nan, babu shakka gaske ne ba a warkewa daga wannan ciwo idan ya yi ƙamari ko ya ta’azzara, amma idan aka garzaya asibiti da wuri kafin ciwon ya gama yi wa mutum illa, za a iya taimaka masa wajen rage ƙarfin ciwon ta hanyar ba shi magunguna, domin ka da mutum ya makance.
Har wa yau, yadda mutum zai san ya na da wannan ciwo na ‘glacoma’ shi ne, idan ya ga yana yawan yin ciwon ido ko ya ga ba ya gani sosai ko ya riƙa ganin hawaye na fita a idanuwansa ko kuma ya ga idanun nasa yana yin ja.
Shi yasa yana da kyau idan mutum ya ji idanunsa na yin ciwo, ya yi maza ya garzaya asibiti, domin a duba a ga mene ne yake damun sa, dalili kuwa wani lokacin za a iyayin zaton ko ciwo ne da aka saba yi yau da kullum a ƙi zuwa asibitin, ba a san cewa; wannan ciwo ba ne da ka iya haddasa makanta ko wani abu mai kama da haka, Allah ya kiyaye mu; amin.
[ad_2]
Source link