Abin fashewa ya tashi a asibiti a Kebbi
[ad_1]
Wani abin fashewa ya yi bindiga a Babban Asibitin Bagudo da ke Jihar Kebbi.
Rundunar ’yan sanda ta ce a safiyar ranar Talata ne abin fashewan ya tashi a wani gidan ma’aikata da ke harbar asibitin.
Kakakin rundunar, SP Bashir Usman Anisma, ya ce rundunar tsaro ta haɗin gwiwa – ’yan sanda, sojoji da ’yan sa-kai – sun isa domin kakkaɓe da kuma tsare wurin da abin ya shafa.
Ya tabbatar da cewa babu wanda ya rasa rai, sai dai wani gini na ma’aikata a cikin asibitin ya lalace, kuma mazaunan wurin an fitar da su lafiya.
SP Bashir Usman Anisma, ya bayyana cewa ƙwararrun masu kula da abubuwan fashewa da sinadarai (EOD-CBRN) suna wurin suna gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sanda ya tura ƙarin jami’an dabarun tsaro domin tabbatar da zaman lafiya, tare da ci gaba da bincike mai zurfi a wurin.
Ya roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da guje wa kusantar yankin da abin ya faru domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da aikin bincike da tsaro yadda ya kamata.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link