’Yan Ta’adda Sun Kai Wa Ƙauyuka 2 Hari A Adamawa

[ad_1]

Wasu da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kai hari ƙauyukan Mubang da Zah da ke Ƙaramar Hukumar Hong a Jihar Adamawa.

Mazauna yankin sun ce maharan sun ƙone gidaje da shaguna yayin harin, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba.

  • An Maka Gwamnatin Tarayya A Kotu Kan Aiwatar Da Dokar Haraji
  • Ɗaliban Nijeriya Sun Nemi A Dakatar Da Dokor Haraji

Wani mazaunin yankin, Mbursa John, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce ba zai iya bayyana adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba.

Ya ƙara da cewa mutane da dama sun tsere zuwa dazuka domin kare kansu, saboda tsoron sake kai musu hari.

Harin ya kawo cikas ga harkokin yau da kullum a ƙauyukan da abin ya shafa, inda kasuwanci ya tsaya tare da raba magidanta da muhallansu.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ƙoƙarin jin ta bakin shugaban Ƙaramar Hukumar Hong bai yi nasara ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *