Amurka za ta hana ’yan Najeriyar da ake zargi da yi wa Kiristoci kisan kiyashi biza
[ad_1]
Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda ya ce Amurka na ɗaukar mataki mai ƙarfi kan munanan ayyuka da tashin hankali da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da sauran sassan duniya.
“Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka (@StateDept) za ta takaita bizar Amurka ga waɗanda suka san da gaske suna jagoranta, ba da izini, ɗaukar nauyi, goyon baya, ko aiwatar da take hakkin ’yancin yin addini. Wadannan manufofin biza sun shafi Najeriya da sauran gwamnatoci ko mutane da ke zaluntar jama’a saboda addininsu,” in ji Rubio.
Maganganun Rubio sun zo ne kwana guda bayan ’yan majalisar Amurka sun gudanar da taron jin ra’ayi a Washington tare da masana kan ’yancin yin addini da dangantakar ƙasashen waje domin tattauna ƙaruwa da tashin hankali a Najeriya da kuma “zaluncin da aka fi karkata ga Kiristoci.”
Taron majalisar ya kasance wani ɓangare na bincike da ake ci gaba da yi kan batun, bisa umarnin Shugaban Ƙasa Donald Trump.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link