Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin
[ad_1]
Alhamdulillahi… kamar yadda muka ga farkon watan Ramadan, Malamai suka yi ta fassara littafin Allah mai girma daidai gwargwadon fahimtarsu, wanda ya aiko fiyayyen Annabinsa, Annabi Muhammad SAW da shi zuwa ga bayinsa, don ya sanar da su ilimin farko da na karshe, ilimin sama da na kasa, ilimin abinda ya bayyana da wanda ya buya, ilimin sanin halittar ubangiji tun daga farkonta har zuwa karshenta, yau Allah ya nuna mana karshen watan lafiya, muna fata ya yafe mana kura-kuranmu, ya karbi addu’o’inmu, ya nuna mana na badin-badada.
Wannan makon, shafin namu mai albarka, tsakuro mana wasu ilimai da fahimtoci na zamani ya yi, wanda ya dace al’ummar musulmi da kowa ma baki daya ya sani a wannan zamanin.
Ga wasu da muka tsakuro muku:
Duk Abin da ya zo A Alkur’ani, Ilimi Ne Mai Girma Ba Wasa Ba
Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) ya yi kira ga al’ummar musulmi da su rungumi bincike acikin addini, sannan su yi watsi da rikicin akida.
Duba da hakan, Mai Diwani ya lura cewa, Alkur’ani yana dauke da ayoyi fiye da 6,000 amma ayoyin shari’a (Muhkamatu), ba su wuce 200 da wani abu ba, sauran duk bayanin ilimai da halitta suke yi.
Mu yi koyi da Annabi Ibrahim (AS) a bangaren neman ilimi, inda yake cewa, “rabbi arini kaifa tuhyil mauta – ya ubangiji, nuna min yadda kake raya halitta”, ma’ana, neman ilimi sai da tambaya.
Alhamdulillahi, wannan itace dabi’ar Sufanci – Tambaya a ilimi don neman sani, amma tsarin Malaman baya dake cewa, yin tambaya a ilimi neman tayar da husuma ce, wannan ba daidai ba ne.
Ubangiji tabaraka wata’ala, ya nemi Annabi SAW da ya roki karin ilimi, “wa kurrabi zidni ilma – kace, ya Ubangiji kara min ilimi”, sabida ilimin littafinsa yana da yawa da fadi, wani an fahimce shi a zamanin saukarsa, wani kuma za a cigaba da fahimtarsa ne da sauyawan zamani, don haka, duk abin da ya sauka a Alkur’ani sai ya tabbata, ko dai a zamanin Annabi SAW ko a bayansa, da fadin Ubangiji cewa, “la tuharrik bihi lisanaka lita’ajala bihi, inna alaina jam’ahu wa kur’anah”.
Wasu sun bautawa shaidan don kwaikwayon halinsa don samun ilimi, kuma sun samu ilimin mai kyau da mara kyau, don haka, Mai Diwani ya yi kira ga kowa da kowa da ya yi kokari a kan hanyar Allah don samun ilimi mai zurfi.
Kimiyya da fasahar zamani (Technology) ya wayar mana da kai, akan bin Alkur’aninmu.
Tsarin duniya, yana sauyawa, misali a kusa-kusa, daga 2018/2019, zuwa 2025, sannan 2026 ta zo da nata sabon tsarin, duba da tsarukan da gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ke aiwatarwa, wanda ke shirin mayar da duniya tsarin jari hujja da barazanar karfin soji.
Da wannan, ya dace mu koma sabon tsarin da za a tafi a kai, (Alkur’ani), tsarin karatun musulmi ba tafiyar su ba.
Allah Ya Hore Wa Annabi SAW Ilimin Sama Da Na Kasa A Alkur’ani
A rana ta uku, tafsirin ya ci gaba cikin tsari da zurfin ilimi kamar yadda aka fara tun ranar farko da ta biyu.
Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) ya ci gaba da tafsiri a cikin Suratun-Naml, inda ya jaddada muhimmancin sabunta fahimtar addini daidai da zamani, yana mai cewa wannan sabuntawa ita ce hanyar da za ta kawo ci gaba ga duniya da kuma al’ummar Musulmi baki ɗaya.
Girman Annabi SAW da Mu’ujizarsa,
Shehun malamin ya yi bayani mai zurfi kan girman Annabi SAW zahiri da badini, inda ya kawo ilgazai da dalilai masu yawa kan bãdinin Annabi SAW. Ya bayyana cewa babbar Mu’ujizar Annabi SAW ita ce Alkur’ani, wanda Allah ya hore masa dukkan halitta da dukkan ilimin duniya—na kasa da na sama.
Sheikh Mai Diwani ya yi kira ga masu bincike daga Turai da sauran al’umma da su zurfafa bincike domin gano kalimomin ilimin Allah da ke cikin Alkur’ani. A nan ne ya yi karin haske cewa, duk Mu’ujizozin Annabawa da suka gabata, duk da girmansu amma suna bayan Mu’ujizar Annabi SAW.
Misalai daga Annabawa:
Annabi Nuhu (AS): An kawo tarihinsa da Mu’ujizozinsa masu girma, amma an jaddada cewa duk suna bayan Annabi SAW.
Annabi Ibrahim (AS): An bayyana cewa ya zo da ilimi a matsayin hujja; ya fara gano ilimai daban-daban, ya fahimci tafiyar duniya da amfanarta, Allah Ya sanar da shi Ilmul-Yakin, Ainul-Yakin da Hakkul-Yakin, har ya zama mai cikakken yakini. Duk da wannan matsayi, Annabi SAW shi ne jagoransa.
Annabi Musa (AS): Allah Ya ba shi himma wajen tsarin noma da kiwo na zamani, da ’yanci daga Fir’auna—amma a iyakar mutanensa. Amma Annabi SAW ya ba Larabawa karfi, ’yanci da hadin kai, har suka mallaki duniya da kyakkyawar dabi’a—wadda ita ce babbar ni’ima da Allah Ya ba shi. Wannan dabi’ar ce Annabi SAW ya rayu da ita tsawon shekaru 40 kafin a aike shi zuwa ga halitta baki daya.
Annabi Isa (AS): An yi bayani kan saukin shari’arsa, inda ya halatta wa mutanensa wasu abubuwa da aka haramta wa mutanen Annabi Musa (AS).
A yin kira ga Sauki da Hikima, Mai Diwani ya yi kira ga Musulmi da su rika kira ga abubuwa masu sauki da tausasawa ga al’umma, inda ya ce,
“Ba dole a addini.” Da kuma ayar da ke magana kan yaki har sai an yi imani—inda ya jaddada cewa a wannan zamani, Allah ne Mai rarrabewa, shi ne masani kuma Mai iko a kan komai, kuma hikima da adalci su ne mafita.
Da Ilimin Lissafi Aka Bankado Gaibu Har Ta Zama A Bayyane, Komai Zai Yiwu
Mai Diwani, ya cigaba da kwararo karatu, inda ya bayyana cewa, duk wanda ya san falsafa, dole ya yarda da Allah, domin akwai wani abu da ya fi karfin danAdam. Allah bai halicci danAdam domin ya boye masa komai daga gaibu ba. Ya kara da cewa, babbar surar da ta yi magana a kan gaibu, ita ce Suratul Jinn, inda Allah ya bayyana cewa yana sanar da wanda ya yarda da shi daga cikin manzanni domin su isar da sakonsa ga jama’a. Komai na Ubangiji a lissafe yake don shi ne mai kiyaye lissafin komai.
Shehu Mai Diwani ya kawo misalai na wasu da Allah ya sanar da su wasu abubuwa na gaibu (boye), kamar masana kimiyya ko likitoci da kan gano abubuwan da suke a boye ba a bayyane ba, kuma daga baya hakan ya tabbata. Ya yi kira ga wadanda ba su fahimci ilimin gaibu ba da su guji magana a kan al’amuransa , domin komai yana cikin ilimin Allah, sai dai kaine baka sani ba.
Shehin ya jaddada cewa, kowace kasa idan ta kula da bangaren ilimi da kimiyya da fasaha (science and technology), za ta samu ci gaba a fannoni da dama ciki har da noma da kasuwanci, har ta kai ga sayar da fasahar. Ya ambato maganar Shehu Ibrahim (RTA) cewa idan aka ce malami, ba wai malamin addini kadai ake nufi ba, domin malami shi ne duk wanda ya san wani ilimi daga ilimin Allah da zai kawo ci gaba da wayewa ga al’umma.
Shehin ya kara da cewa, yawancin sauye-sauye da aka samu a fannin fikihu da tafiyar da addini, sun faru ne a zamanin daular Abbasiyya, wadanda suka hada mulki da addini, ba kamar yadda Umawiyawa suka yi ba, duk da cewa su ne suka fara kafa siyasa ta karfi.
Ya bayyana cewa, duk ilimin turawa wani bangare ne dake cikin tulin ilimin Ummul Kitab. Don haka, Mai Diwani ya yi kira da a kawar da kabilanci da wariyar launin fata, wanda yace, Isr@’1la, itace kasar da tafi nuna wariya, don haka ta rasa kasa mallakin kanta, sai dai tsilla-tsilla.
An kuma yi bayani cewa Annabi (SAW) shi ne ya rufe annabta bayan ya cika kyawawan dabi’u, ya kawo sauyi da ci gaba a rayuwar al’umma, ya yaki kabilanci, bokanci da karya. A yanzu babu wahayi sai dai ilhama ga wanda ya bi Allah da gaskiya.
Sayyidina Ali (KRM) ya ce duk wata bidi’a yawanci daga malamai take fitowa ta hanyar kirkirar abubuwan da ba su da asali a addini.
An bayyana cewa, Allah ya bai wa Annabi (SAW) Akalul A’ala, ya haskaka zuciyarsa ta hanyar zikiri, salla, tafakkuri da tadabburin Alkur’ani. Allah Ya zabi watan Ramadan domin saukar da Alkur’ani, ciki har da Suratul Fatiha wadda ita ce mabudin alheri da ni’ima.
Shehu Mai Diwani ya kara da bayanin ma’anar “An’amta Alaihim” da “Maghdubi Alaihim” a cikin Suratul Fatiha, yana mai cewa “An’amta Alaihim” su ne masu kyawawan dabi’u, yayin da “Maghdubi Alaihim” su ne marasa kyawawan dabi’u. Ya jaddada cewa ba a takaita wannan ma’ana ga wata kabila ko addini kadai ba, sai dai halayen mutum ne suke zama mizani.
[ad_2]
Source link