NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya

[ad_1]



Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP) shiyyar Kano, ta kama wani mutum da ya yi yunƙurin safarar wasu mata bakwai zuwa Saudiyya.

Jami’an NAPTIP sun kai samame wani gida a Kano a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2025, bayan samun bayanan sirri, inda aka ɓoye matan da ake shirin safararsu.

A cewar Mohammed Habib, Jami’in Hulɗa da Jama’a na NAPTIP a Kano, an ajiye matan a gidan ne yayin da ake shirin tura su Saudiyya domin yin aikatau.

Ya ce, “Bincike ya nuna cewa biyu daga cikin waɗanda aka ceto ’yan Nijar ne, yayin da biyar kuma ’yan Najeriya ne.”

Ya ƙara da cewa, “An kai matan Accra a Ghana, inda aka yi musu biza. Kuma duka aikin da za a musu bashi ne, inda kowacce za ta biya Naira miliyan 10, idan sun yi aikin wahala a Saudiyya .”

NAPTIP ta bayyana cewa an riga an kammala shirin tura matan filin jirgin saman Abuja a ranar 3 ga watan Disamba, 2025, wanda a nan aka shirya tafiyarsu Saudiyya.

Hukumar ta ce an kama mutum ɗaya, yayin da sauran waɗanda ke da hannu a lamarin suka tsere.

Jami’in, ya tabbatar da cewa hukumar na ci gaba da bincike domin kama sauran da suka tsere.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *