Imam Abdullahi Abubakar, Wanda Ya Boye Kiristoci 300 A Rikicin Filato Na 2018, Ya Rasu

[ad_1]

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Imam Abdullahi Abubakar, wanda ya shahara a duniya saboda kare ɗaruruwan Kiristoci a lokacin hare-haren addini da suka auku a Jihar Filato a shekarar 2018, ya rasu yana da shekaru 92. Marigayin, wanda shi ne Babban Limamin ƙauyen Nghar da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi, ya rasu bayan gajeriyar jinya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Imam Abubakar ya yi fice ne a ranar 23 ga Yuni, 2018, lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai hari kan al’ummomi da dama a Barkin Ladi, inda mutane da dama suka rasa rayukansu. A cikin wannan rikici, ya buɗe masallacinsa da gidansa domin bai wa aƙalla Kiristoci 300 mafaka, inda ya ƙi miƙa su ga maharan. A wancan lokaci, ya ce ya aikata hakan ne bisa koyarwar addininsa na kare rayukan mutane ba tare da la’akari da addini ba.

  • Ana Ci Gaba Da Alhinin Mutuwar Malam Adamu Fika
  • ‘Yan Bindiga Sun Rage Kuɗin Fansar Matafiya 28 Da Suka Sace A Filato zuwa N30m

Wannan jarumtaka ta sa ya samu karramawa daga cikin gida da wajen ƙasa. Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar girmamawa ta OON, yayin da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba masa a bainar jama’a. Haka kuma, ƙungiyar LEADERSHIP Media Group ta zaɓe shi a matsayin wanda ya yi nasara tare da Alhaji Aliko Dangote a lambar “Mutumin Shekara.” A shekarar 2019gwamnatin Amurka ta ba shi lambar International Religious Freedom Award, inda ta bayyana shi a matsayin “ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kai tsakanin addinai.”

Da yake jimamin rasuwarsa, Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana marigayin a matsayin “alamar zaman lafiya, haɗin kai da shugabanci na sadaukarwa.” Ya ce mutuwarsa babbar rashi ce ga iyalansa, al’ummarsa da jihar baki ɗaya, yana mai kira ga jama’a da su ci gaba da riƙe ƙa’idojin tausayi, haƙuri da zaman lafiya da Imam Abdullahi Abubakar ya bari a matsayin gado.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *