Goron Juma’a 16-01-2026

[ad_1]

Jama’a barkanmu da juma’a, barkanmu da kasancewa tare da wannan shafin na GORON JUMA’A, shafin da yake bawa kowa damar miƙa saƙon gaishe-gaishensa zuwa ga ƴan’uwa da abokan arziƙi, na kusa da na nesa, har ma da waɗanda aka daɗe ba a haɗu ba.

Kamar kowane mako, yau ma shafin na tafe da wasu saƙonnin gaishe-gaishen da ku ka aiko mana kamar haka:

Saƙo Daga Rahma Ibrahim Maƙarfi, Jihar Kaduna:

Ina gaishe da ƙawayena Salma Ahmad, Zainab Haruna, Maimuna Usman, Maryam Isyaku, Suwaiba Idris, Aisha Ibrahim, Fauziyya Ibrahim, Mariya Hassan, Salma Salisu, Hafiza Yunusa, Mubaraka Auwal, Walida Sa’id. Sannan ina gaishe da iyayena da sauran ƴan uwana na gida da fatan za su yi juma’a lafiya.

  • GORON JUMA’A 05/12/2025
  • GORON JUMA’A 12/12/2025

Saƙo Daga Muhammad Usman, Jihar Katsina:

Ina miƙa saƙon gaisuwata zuwa ga babban abokina Saleh, da sauran abokaina kamar su; Ahmad Idris, Yunusa Ibrahim, Habibu Hassan (Bn Hassan), Tasi’u Muhammad, Salisu Shitu (ɗan borno), Habibu Ɗan Iliya, Nasiru Yaro, da masoyiyata abar ƙaunata Zainab Zee-zee, da mahaifana, da ƙannena da yayyena, da fatan za su yi juma’a lafiya.

Saƙo Daga Mardiyya Ahmad Dikko, Jihar Katsina:

Assalamu Alaikum, saƙon barka da juma’a zuwa ga ma’aikatan gidan jaridar Leadership, musamman me gabatar da wannan shafi Rabi’at Sidi Bala, Edita Hamza Bello, da kuma sauran ma’aikatan kuna burge ni wallahi, Allah ya sa ku fi haka, ya kuma kare ku daga sharrin masu sharri, ya ƙara ɗaukaka gidan jaridar Leadership Hausa a duniya. Ina gaishe da yarana Sa’ad, fauziyya, da Al’amin, Sumayya, Faisal da kuma maigidana Alhaji Mu’azzam Idi Yari Allah ubangiji ya Albarkace su.  Da fatan sun yi sallar juma’a lafiya.

Saƙo Daga Hafsat Adam Isah, Jihar Kaduna:

Dan Allah jaridar Leadership a miƙan saƙon gaisuwata zuwa ga ƙawata rabin raina Fatima Isah, da kuma Aisha Lawan, da Suwaiba Abdulmuminu, da Sa’adatu Sale, da ƴan group ɗin ‘Chapter Sƙuad’ irin su; Lily, Zulaihat, da sauran na ciki kowa da kowa. Sai kuma gaisuwa zuwa ga Idris Saminu (Ɗan Baba), da yayana Kabir Adam, ƙanwata Amina Adam, ƙaramar ƙanwarmu Safiyya Adam, da kuma Mamana Hajiya Amina Ɗahiru Wada, da Abbana Alhaji Adamu Gidaje.

Saƙo Daga Shafa’atu Tijjani Doguwa, Jihar Kano:

Assalamu Alaikum  Ina miƙo saƙona na gaisuwa zuwa ga Umar Hamza (Asasanta), ina gaishe shi, da ƙawayena Umaima Sulaiman da Bilkisu Ibrahim, da Zarah Abubakar da Aisha Hamza da sauran ƙawayena na islamiya dana boko, Allah ya sa za su yi juma’a lafiya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *