Ruwan wuta ya sa ’yan bindiga sun fara neman sulhu a Kogi – Gwamnati

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Kogi ta ce wasu ’yan bindiga sun fara neman tattaunawa domin su ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya sakamakon ruwan wutar da ake musu.

Mai ba Gwamnan jihar shawara kan tsaro Kwamanda Jerry Omodara (mai ritaya), ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a Lokoja, babban birnin jihar ranar Juma’a.

Ya ce wannan mataki ya biyo bayan hare-haren da ake kai wa ’yan bindigar, ciki har da ruwan wuta a maboyarsu da rushe gidajen da suke amfani da su wajen aikata laifuka a wasu sassan jihar.

Omodara ya ce gwamnatin jihar, karkashin Gwamna Usman Ododo, ta yi amfani da fasaha wajen yaki da rashin tsaro a cikin shekaru biyu da suka gabata, lamarin da ya taimaka wajen fin karfin ’yan ta’adda da ke addabar al’umma.

“Ku tuna cewa a jawabin rantsuwarsa a ranar 27 ga Janairu, 2024, Gwamna Ododo ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Daya daga cikin karfin gwamnati shi ne amfani da fasaha, kuma shirin kara amfani da ita yana kan gaba domin kai wa ’yan ta’adda farmaki a daji,” in ji shi.

Ya kara da cewa an samar da motocin Hilux, Siena da babura ga Sojoji, ’yan Sanda, JTF da ’yan sa-kai domin inganta ayyukansu wajen yaki da ’yan ta’adda.

A cewarsa, daya daga cikin manufofin gwamnati shi ne kin tattaunawa da ’yan ta’adda, tare da ci gaba da kai musu farmaki a maboyarsu.

Omodara ya kara da cewa ana shirin kafa dokar da za ta haramta zama a daji, inda ya ce duk wanda zai zauna a Kogi dole ne ya zauna a gari ko wurin da aka sani.

Ya bayyana cewa banda ’yan bindigar da ke kaura daga Arewa saboda ruwan wuta, an gano wasu ’yan cikin gida da ke taimaka musu wajen aikata laifuka.

“Duk ’yan bindigar da abokan aikinsu na cikin gida suna dandana kudarsu yayin da gwamnati da jami’an tsaro ke ci gaba da kai musu farmaki ba tare da sassauci ba,” in ji shi.

Duk da karuwar ayyukan ’yan ta’adda, Omodara ya jaddada cewa Kogi ce jiha
mafi aminci a Arewa ta Tsakiya, yana danganta nasarar da tattara bayanan sirri da kuma kyakkyawar aniyar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Ododo suka nuna.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *