Kotu Ta Yi Wa Wani Mutum Bulala, Ta Tura Shi Makarantar Islamiyya A Kano

[ad_1]

Kotun Shari’ar Muslunci a Jihar Kano da ke zamanta a Kofar Kudu ta yankewa wani mai suna Khalifa Auwal hukuncin yin aikin al’umma na tsawon watanni shida, bayan samunsa da laifin kutse da kuma sata.

A cewar kotun, a cikin wannan lokaci, Auwal zai kasance yana karatun addinin Musulunci a wata makarantar Islamiyya a matsayin wani ɓangare na shirin gyara tarbiyyarsa.

  • Kano Za Ta Horar Da Matasa 50,000 A Shirin Koyon Sana’o’i
  • Kotu Ta Yanke Wa Masu Barkwanci 2 Hukuncin Bulala 40 A Kano

Lauyan gwamnati ya shaida wa kotun cewa an kama wanda ake tuhuma ne yayin da yake yanke sandunan ƙarfe a wurin ginin gadar Tal’adu da ke Gudale, a ƙaramar hukumar Gwale, inda ake zarginsa da aikata laifin kutse da sata. Auwal ya amsa laifinsa a gaban kotu ba tare da gardama ba.

A hukuncinsa, Alkali Shamsuddeen Ado Abdullahi Unguwar Gini ya bayar da umarnin a yi wa wanda aka yanke wa hukunci bulala 50 tare da ɗora masa aikin al’umma na watanni shida, sannan ya umarce shi da yin karatun Fiqhu (ilimin shari’ar Musulunci) ƙarƙashin kulawar Audu Dan Hajiya, jami’in kotu, domin gyara halayensa da dawo da shi hanya madaidaiciya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *