Ƙungiyar Miyetti Allah Ta Musanta Zargin Amurka Kan Kisan Kiristoci
[ad_1]
Ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta ce ba ta da hannu a kisan Kiristoci a Nijeriya, bayan Amurka ta saka sunanta cikin jerin waɗanda ake tunanin ƙaƙaba wa takunkumi.
Shugaban ƙungiyar, Baba Othman Nganzerma, ya ce ƙungiyar ƙwararrun makiyaya ce kawai wadda ke kare muradun mambobinta, kuma ba ta riƙe makamai ko ɗaukar nauyin hare-hare.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Amsa Tambayoyin Manema Labaru
- Haƙƙin Ɗan’adam Na Fuskantar Mummunar Barazana A Duniya – Guterres
Ya bayyana cewa mambobin ƙungiyar sun fito daga ƙabilu da addinai daban-daban, don haka bai dace a ɗora laifin wasu mutane a kan ƙungiyar gaba ɗaya ba.
Ƙungiyar ta ce ta aika wasiƙa ga hukumomin Amurka domin fayyace matsayarta, tare da jaddada cewa tana aiki tare da jami’an tsaron Nijeriya.
A cewarta, rikice-rikicen da ke faruwa a ƙasar sun fi alaƙa da taƙaddama kan mallakar filaye da albarkatun ƙasa, ba batun addini ko ƙabilanci ba.
Ƙungiyar, wadda aka fi sani da Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), an kafa ta a matsayin ƙungiyar ƙasa tun a shekarar 1986.
[ad_2]
Source link