Amurka Ta Sanya Kyautar Ladan Dala Miliyan 10 Kan Bayanin Shugabannin Sojin Iran
[ad_1]
Gwamnatin Amurka ta sanar da bayar da ladan da ya kai dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan wasu manyan jami’an soji da na leƙen asirin Iran, ciki har da sabon jagoran ƙasar, Ayatollah Mojtaba Khamenei.
A cewar bayanan da aka wallafa a shafin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, ladan ya shafi jami’ai 10 da ake dangantawa da Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC), rundunar sojin Iran da aka kafa bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979 domin kare tsarin mulkin addini na ƙasar.
- An Kama Na Hannun Daman Ganduje Kan Badaƙalar ‘Dala Dry Port’ A Kano
- Kamfanin Shell Ya Yi Alƙawarin Zuba Jarin Dala Biliyan 20 A Najeriya Bayan Dala Biliyan 7 Da Aka Kashe – NNPCL GCEO
Rahotanni sun ce Mojtaba Khamenei ya gaji mahaifinsa, Ali Khamenei, a matsayin jagoran ƙasar bayan mutuwarsa tare da wasu manyan jami’an Iran a hare-haren haɗin gwuiwa da Amurka da Israel suka kai tun daga ranar 28 ga Fabrairu.
Sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa Ali Larijani ya bayyana a wani gangami a Tehran tare da shugaban ƙasar, Masoud Pezeshkian, da ministan harkokin waje, Abbas Araqchi, duk da iƙirarin da sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya yi cewa shugabannin Iran suna ɓoye a karkashin ƙasa.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce waɗannan jami’an na jagorantar sassan IRGC da ke tsarawa da aiwatar da hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban na duniya. Sai dai Iran ta daɗe tana musanta zargin tallafa wa ta’addanci, tana mai cewa zarge-zargen na Amurka siyasa ce da ake amfani da ita wajen ƙara matsin lamba ko kakaba takunkumi a kan ƙasar.
[ad_2]
Source link