An kashe jami’in Sibil Difens a wurin rabon tallafin Alhassan Doguwa a Kano
[ad_1]
Ajali ya kaste hanzarin wani jami’in hukumar tsaro ta Sibil Difens a wajen rabon tallafin kayayyakin azumi da na sallah a Karamar Hukumar Tudun Wada ta Jihar Kano.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’a yayin da ake rabon tallafin wanda ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa ya ɗauki nauyin raba wa al’ummar yankin.
Da yake tabbatar da lamarin, ɗan majalisar ya ce jami’in ya rasu ne a yayin da wasu ɓata-gari suka yi yunƙurin tayar da tarzoma a wurin tabon tallafin.
Alhassan Doguwa ya bayyana alhininsa kan lamarin, inda ya miƙa ta’aziyyarsa ga hukumar sibil difens da iyalan mamacin da kuma al’ummar Tudun Wada baki ɗaya.
Ya buƙaci jami’an tsaro da su gaggauta gudanar da bincike domin bankaɗo masu hannu a wannan aika-aika da ya ce tilas ne su fuskanci fushin doka.
Doguwa ya kuma gargaɗi masu yaɗa jita-jitar da ke alaƙanta shi da rasuwar jami’in, yana mai jaddada cewa zai ɗauki matakin shari’a kan duk wani da ya yi yunƙurin ɓata masa suna ko ta mazaɓar da yake wakilta.
Ya yi adduar Allah Ya jiƙan mamacin, tare da nanata buƙatar a riƙa lura a kowane wuri na taron jama’a.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link