Bayan Ganawa Da Tinubu, Gwamna Abba Zai Iya Komawa APC A Talata Ko Laraba

[ad_1]

A yayin da ake ta raɗe-raɗin yiwuwar sauya sheƙa, Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Litinin.

Taron da aka yi a sirrance, ya haifar da jita-jitar cewa gwamnan, wanda aka zaɓa a karkashin jam’iyyar NNPP yana shirin komawa Jam’iyyar APC.

  • Binciken CGTN: Tattalin Arzikin Sin Ya Samar Da Tabbaci Ga Tattalin Arzikin Duniya Mai Cike Da Sauye-Sauye
  • Hainan Ta Karbi Karin Masu Bude Ido Daga Ketare

A yayin da aka nemi jin ta bakinsa, Gwamnan ya ki yin wani tsokaci lokacin da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa suka tuntuɓe shi bayan ganawar da ya yi da Shugaban Kasa.

Akwai rahotanni masu cewa, sauya shekar gwamnan ta fuskanci matsala bayan da APC ta ki amincewa da bukatarsa ​​ta bashi tikitin takarar gwamna kai tsaye kafin zaɓen gwamna na 2027.

A halin yanzu, shugaban APC a Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya nuna cewa Gwamna Yusuf zai iya yin rijista a hukumance tare da karɓar katin zama dan jam’iyyar tsakanin ranar Talata da Laraba a wannan makon.

Abbas ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga kimanin ma’aikatan wucin gadi 1,500 da jam’iyyar ta ɗauka don gudanar da aikin rajistar zama dan jam’iyyar ta hanyar amfani da intanet (e-register) a fadin jihar.

A cewarsa, an jinkirta fara rajistar ne domin bayar da damar dawowar tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da gwamna Abba daga Abuja, inda suka ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *