Gwamnan Kano Ya Yi Allah-wadai Da Kisan Uwa Da ‘Ya’yanta 6, Ya Umarci A Kamo Masu Laifin
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya yi Allah-wadai da kisan wata mata da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano a ranar Asabar, inda ya bayyana lamarin a matsayin rashin hankali da kuma cin mutuncin ɗan adam.
A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sunusi Bature ya fitar a ranar Asabar, gwamnan ya nuna matukar bakin ciki game da wannan bala’i sannan ya mika ta’aziyya ga iyalan da suka rasu, mazauna Dorayi Chiranchi, da kuma dukkan mutanen Jihar Kano.
- Fitaccen Ɗan Kasuwar Kano, Bature Abdulaziz, Ya Rasu
- Mutum 10 Sun Shiga Hannu Bisa Zargin Fashi Da Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Jigawa
Gwamna Yusuf ya bayyana kisan a matsayin abin da ba za a lamunta ba, kuma ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an gurfanar da waɗanda ke da hannu a gaban kotu.
Ya umarci Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano da ta fara farautar waɗanda suka aikata wannan aika-aika nan take da nufin kamawa da gurfanar da su, yana mai gargaɗin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci cikakken hukunci.
An ruwaito gwamnan yana cewa, “Gwamnati ba za ta ƙyale waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi ba, ba tare da an hukunta su ba.”
[ad_2]
Source link