Fitaccen ɗan kasuwa a Kano, Bature Abdulaziz ya rasu

[ad_1]



Wani fitaccen ɗan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji Bature Abdulaziz ya ras a yammacin jiya Asabar bayan fama gajeriyar rashin lafiya.

Babban ɗansa, Abdulaziz Bature Abdulaziz ne ya sanar da rasuwar mahaifin nasu da ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekaru 76 a doron ƙasa.

Aminiya ta ruwaito cewa za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 10 na safiyar wannan Lahadin a gidansa da ke unguwar ’Yan Kaba a Jihar Kano.

Marigayin ya riƙe muƙamai daban-daban da suka haɗar da shugaban ƙungiyar ’yan kasuwa ta Harmonizes Traders Union of Nigeria, HTUN.

Kazalika, ya riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar dattawa masu kishin ƙasa da da’awar zaman lafiya ta Patriotic Elders Network for Peace.

Bature Abdulaziz ya kuma shahara a nan cikin gida musamman lokacin da ya riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar ’yan kasuwar Kantin Kwari da ke ƙwaryar birnin Dabo.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *