Matar aure ta yanka wuyan mijinta, ta fasa masa ido da wuƙa a Neja
[ad_1]
An kama wata matar aure a garin Kuta, hedikwatar Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, bisa zargin yankar wuyan mijinta, Salisu Suleiman, da wukar girki.
Majiyoyi sun ce matar ta kuma soka wa mijin wuka a idonsa na hagu, lamarin da ya lalata idon gaba ɗaya.
Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta bayyana wa wakilinmu cewa ma’auratan sun samu saɓani ne, inda matar ta jira har sai da mijin ya kwanta barci kafin ta kai masa hari da wuƙa.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce lamarinya auku ne da safiyar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025.
A cewarsa, “A ranar 1 ga Nuwamba, da misalin ƙarfe 2:30 na asuba, wani Salisu Suleiman na garin Kuta ya samu saɓani da matarsa, Halima Salisu, inda da mijin ya kwanta barci, matar ta ɗauki wuƙa ta yankar masa wuya, sannan ta soka masa a idon hagu.”
SP Abiodun ya ce an garzaya da wanda abin ya faru da shi Asibitin Gabaɗaya na Kuta, daga nan kuma aka mayar da shi Asibitin Ƙwararru na IBB da ke Minna domin ƙarin kulawar likitoci.
Ya ƙara da cewa, “An kama wadda ake zargi, kuma tana tsare a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link